An sanar da cewa magajin garin New York, Bill de Blasio ya watsawa Saudiyya kasa a ido inda ya bayyana cewa ba zai halarci taron "Urban 20" akan bunkasa birane da Saudiyya ta shirya ta yanar gizo ba kasancewar yadda kasar ke ci gaba da take hakkokin bil adama.
Blasio, ya bayyana cewa ba zai halarci taron da Saudiyyar ta shirya ta yanar gizo tsakanin 30 ga watan Satumba zuwa 2 ga watan Oktoba sabili da zargin take hakkokin bil adama.
A yayinda yake bayyana cewa ba zai halarci taron da Saudiyya ta shirya ba sabili da take hakkokin bil adama da kasar ke yi, ya bayyana cewa bai kamata mu kasance shugabannin da bamu magana domin kalubalantar rashin adalci ba.
Blasio, ya yi kira da ayi hadaka gurin sulhu da kare hakkokin bil adama inda ya yi kira da sauran takwarorinsa da su janye daga taron da Saudiyya ta shirya.
Blasio ya kara da cewa ya kamata a kauracewa taron sabili da tunawa da zagayowar shekara ta biyu da kisan dan jarida Jamal Kashoggi. Inda ya kara da cewa taron yazo dai-dai da ranar da aka kashe Jamal Kashoggi shekaru biyu da suka gabata.
Saudiyya a ranar 2 ga watan Oktoban shekakar 2018 ta kashe dan jarida Jamal Kashoggi a ofishin jakadancinta dake Istanbul.