An fara kamfen din tsabtace da sake gina Zirin Gaza da taken "Zamu sake gina Zirin Gaza", inda mummunar barna ta faru saboda tsananin ruwan bama-bamai na kwanaki 11 da Isra'ila ta aikata.
Kimanin matasa dubu daya ne suka halarci kamfen din da ofishin magajin garin Gaza ta kaddamar.
A cikin rubutaccen bayanin nasa, Magajin garin Gaza Yahya es-Serrac ya bayyana cewa suna son kawar da tasirin hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a yankin tare da bayar da sakon cewa Gaza na da karfin da ‘ya’yanta za su iya sake ginata.
Da yake bayyana cewa kamfen din da ake magana a kansa ya fara ne a jiya, Serrac ya bayyana cewa suna da niyyar sake farfado da Gaza tare da wannan kamfen da goyon bayan dukkan bangarorin al'umma.
Magajin garin, Serrac ya bayyana cewa kamfen din "Zamu Sake Gyara" zai dauki makonni biyu ana yi.