Macron na buƙatar 'maganin tabin hankali'

Macron na buƙatar 'maganin tabin hankali'

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa takwaransa na Faransa Emmanuel Macron ba bukatar maganin tabin hankali ganin irin kiyayyar da yake nunawa Musulunci.

Erdoğan, dake jawabi a taron kolin jam'iyyarsa na AK Parti karo na 7 a garin Kayseri ya bayyana cewa,

"Menene matsalar mutumin da ake kira Macron da Musulunci, me ya hada shi da Musulmai?"
Erdoğan, ya kuma kara da cewa,

"Macron na bukatar maganin tabin hankali. Menene za mu iya kara cewa akan mutumin da bai san 'yancin addini ba, wanda ke irin wannan daukar matakin ga wasu addinan dake zaune a kasarsa. Da farko dai ya kamata ka duba hankali. Na biyu kuma kana kokarin yin gwagwarmaya da Erdoğan, gwagwarmaya da  Erdoğan ba zai amfanar da kai da komai ba. Bayan shekara daya dai akwai zabe, bayan zaben zamu gani, bani tunanin hanyar ka za ta kasance mai dorewa ba.

 


News Source:   ()