Mace ta farko da ta fara tuka jirgin yakin NATO

Mace ta farko da ta fara tuka jirgin yakin NATO

Leman Bozkur Altincekic da aka haifa a shekarar 1933 ce ta samu kambin mace matukiyar jiragen saman Turkiyya da Kawancen NATO ta farko.

Tun Altincekic tana ‘yar karama ta ke da burin tuka jirgin sama, kuma a lokacin da ta gama sakandire ta dauki babban matakin cimma burinta inda ta samu horon tukin jirgi a Sansanin Inonu na Turkushu. Bayan daukar matakin diban mata zuwa rundunar sojin saman Turkiyya a shekarar 1954, sai ta mika takardunta don shiga Kwalejin yakin Sama da ke Izmir a shekarar 1955 inda ta fara karatu a watan Oktoban shekarar. A shekarar 1957 ta kammala samun horon iya tuka jirgin sama mai fanka. A wannan lokaci kawancen NATO mafi girma a duniya na da shekaru 5 a kafuwa.

Leman Bozkurt Alticekic ta samu horon tuka manyan jiragen yaki don bukatarta na tuka irin su. Ta dauki shekaru 9 tana yawo a sararin samaniya, kuma ta zama ita ce mace ta farko da ta fara tuka jiragen saman yaki na Turkiyya da na Kawancen NATO.


News Source:   ()