Ma’aikatan jin ƙai na MDD 207 aka kashe tun bayan fara yaƙi a Gaza

Ma’aikatan jin ƙai na MDD 207 aka kashe tun bayan fara yaƙi a Gaza

Sakatare Janar na majalisar ɗinkin duniya Antonio Gutteres ne ya tabbatar da wannan alƙaluma, ya ce suna buƙatar a hukunta wanda suke da hannu ta hanyar shari’a.

A wani sako da ya wallafa a shafin X shugaban hukumar kula da ƴan gudun hijira ta majalisar ɗinkin duniya dake aiki a Falasɗinu Philippe Lazzarini ya tabbatar da wannan batu.

Sama da ma’aikatan jin ƙai 280 aka kashe a duk faɗin duniya a shekarar 2023 a watanni 3 na farkon fara yaƙin Isra’ila da Falasdinu kamar yadda majalisar ɗinkin duniya ta tabbatar.

Ƙaruwar mutuwar ya zo ne bisa hare-hare ta sama da Isra’ila ta zafafa a Gaza tsakanin watan oktoba zuwa disambar bara.

Wannan ya ƙara adadin ma’aikatan jin ƙai na majalisar ɗinkin duniya da aka kashe da kaso 137 idan aka kwatanta da na shekarar 2022 inda a wannan shekara aka kashe mutum 118.

Ofishin kula da ayyukan jin ƙai na majalisar ɗinkin duniya a ranar litinin ya ce an kashe ma’aikatan jin ƙai a ƙasashe 33 a duniya, kuma wannan ya sa shekarar ta zama wadda aka fi kashe ma’aikatan.

To sai dai acewar ofishin wannan shekarar ka iya zama mafi muni duba da tuni aka hallaka ma’aikatan jin ƙai 172 daga farkon shekarar 2024 zuwa 7 ga Agusta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)