Ma'aikatar Tsaron kasar Turkiyya (MSB) ta yi bikin tunawa da wadanda aka kashe a kisan kare dangin Srebrenica, wanda a kwanan aka bayyana a matsayin mafi munin bala'in da ya taba afkawa al'umma a Turai.
A cikin sakon da Ma'aikatar ta wallafa an bayyana cewa,
"Muna tunawa da shahidanmu a Srebrenica, wadanda aka yi wa kisan gilla a tsakiyar Turai shekaru 26 da suka gabata, kuma muna taya 'yan uwanmu a Bosnia bakin cikin . Ba mu manta ba, ba za mu bari a manta ba .."