Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta fitar da sanarwa kan soke NAVTEX

Kakakin yada labarai na Ma’aikatar Tsaron Kasa (MSB), kwamandar rundunar sojojin ruwa Sebnem Aktop ta sanar da cewa an soke Navtex biyu (sanarwa ga matukan jiragen ruwa) wadanda suka zo daidai da ranakun kasa sakamakon daidaituwa da aka samu.

A sanarwar da Ma'aikatar ta fitar, Aktop ta yi bayani game da soke Navtex.

Inda ta bayyana cewar Turkiyya a koyaushe tana aiki ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa da kyakkyawar dangantakar maƙwabta game da matsalolin yankin Aegean da Gabashin Bahar Rum kuma tana goyon bayan samun maslaha ta hanyar tattaunawa cikin aminci da girmama juna.

Dangane da yarjejeniyar fahimta da aka sanya hannu tsakanin Turkiyya da Girka a Athens a shekarar 1988, an bayyana cewar ba za a yi aiki a cikin ranakun hutun ƙasa da na addini na juna ba a cikin Tekun Aegean da lokacin yawon buɗe ido tsakanin 15 ga Yuni da 15 ga Satumba. Ta tunatar da cewa a ranar 29 ga Satumba, Girka ta sanar da shirin Navtex da za a gudanar da horo na harbi a cikin Tekun Aegean a ranaku ciki har da ranar 29 ga Oktoba, Ranar Jamhuriya ta Turkiyya.

Turkiyya ta mayar da martani yayin da ta sanar da shirin Navtex na gudanar da horo na harbi a ranaku ciki har da ranar 28 ga Oktoba, Ranar hutu ta kasar Girka.

A ranakun 22 zuwa 23 ga Oktoba, Ministan Tsaronmu Hulusi Akar a taron Ministocin Tsaro na NATO da aka yi tare da halartar ministocin tsaro daga kasashe mambobin NATO 30, ya bayyana cewar Turkiyya za to soke shirinta na Navtex na 28 ga Oktoba idan Girka ta soke nata shirin na 29 ga Oktoba. Sakamakon daidaituwa da aka samu, an soke Navtex din biyu da aka shirya gudanarwa a ranakun ƙasa. Bugu da kari, Turkiyya don nuna alamar kyakkyawar niyya, a baya ma ta soke shirin Navtex da ta shirya gudanarwa a yankin Antalya. Tare da cika alkawurransu a karkashin NATO, bayan tattaunawa tsakanin Shugaba Recep Tayyip Erdogan da Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg, Turkiyya ta ci gaba da nuna matsayinta na samun mafita ta hanyar tattaunawa.

Tare da jaddada cewa Sojojin Turkiyya na ci gaba da rakiya tare da kare duk jiragen ruwa na bincike da haka da ke aiki a tekun Bahar Maliya da Gabashin Bahar Rum, Aktop ta ce,

Jirgin binciken namu na Oruc Reis yana ci gaba da aiyuka a cikin takammammen lokaci yada muka tsara a cikin bangarenmu ta nahiyar.


News Source:   ()