Ma'aikatan jirgin ruwa 'yan kasar Ukraine da aka yi garkuwa dasu a Najeriya sun koma kasarsu
Shugaban kasar Ukraine Vladimir Zelenskiy ya karbi tarbi ma'aikatan jirgin ruwa 6 ‘yan kasar Ukraine wadanda aka kame a yankin ruwan Najeriya a ranar 16 ga watan Disamba, 2020.
Kamar yadda shugaban kasar ya bayyana an kaisu Kiev bayan tasowa dasu da aka yi daga Lagos zuwa Istanbul.
Zelenskiy, da yake jawabin tarbon ma'aikatan ya yi nuni ga yadda kasar ke bada da muhinmanci akan 'yan kasarta.
AN dai yi garkuwa da ma'aikatan jirgin ruwan su 8 da suka hada da 'yan kasar Ukraine 6 bayan harin da 'yan fashin teku suka kaiwa jirgin ruwa mai suna "Stevia" a ranar 16 ga watan Disamban 2020.
Zelenskiy, ya kara da cewa an kubutar da ma'aikatan a ranar 31 ga watan Janairu.