Ma'aikata a Lebanon sun tsunduma yajin aiki

Ma'aikata a Lebanon sun tsunduma yajin aiki

An gudanar da yajin aikin gama-gari na kwana daya a Labanon yayin da mutanen ke zanga-zangar tare da neman "gwamnatin ceto"

Bayan kiran da kungiyar kwadagon ta Labanon ta yi, da yawa daga cikin cibiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu sun sanar da kudurinsu na shiga yajin aikin.

Masu zanga-zangar, wadanda suka mayar da martani ga ‘yan siyasar da ba za su iya amincewa da kafa sabuwar gwamnati ba duk da tabarbarewar rikicin tattalin arziki, sun nemi a kafa " gwamnatin ceto "da wuri-wuri domin kubutar da kasar daga halin da take ciki.

 Sun kuma rufe hanyoyin zuwa Beirut babban birnin kasar da sauran yankuna na dan lokaci.

Shugaban kungiyar Kwadago Bashar al-Asmer, a wani taron manema labarai tare da gungun masu fafutuka da suka taru a gaban ginin kungiyar a Beirut, ya yi jawabi ga kungiyoyin siyasa da ba su iya cimma matsaya kan kafa sabuwar gwamnati ba kusan shekara guda.

Esmer ya yi kira ga kungiyoyin siyasa a kasar da su "kafa gwamnatin ceto" ta hanyar daidaito, su daina zargin juna ko bata lokaci a ayyanar da ayyuka a kasar.


News Source:   ()