Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa a yayinda mafi yawancin kasashen duniya suka rungume hannu, Turkiyya ba za ta taba yin shiru ba a cin zarafin da Isra’ila ke yiwa Falasdinawa.
Ya kara da cewa wadanda suka zabi sun sa ido su kyale cin zarafin da Isra’ila ke yiwa Falasdinawa su sani cewa wata rana zata kansu. Inda ya yi kira ga kasashen duniya da su kalubalanci zaluncin da Isra’ila ke aikatawa a Gaza.
Erdogan ya kara da cewa “Ya zama wajibi ga Majalisar Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakan da suka dace domin samr da zaman lafiya a Jarusalam. Inda ya kara da cewa wadanda suka sanya ido ko suka goyi bayan zubar da jinin da Isra’ila ke yi su sani cewa wata rana kansu za’a fado.
“Harin da ta kaiwa gurin ibada mai tsarki ga addinai uku, lamari dake nuna kasar ta’addanci Isra’ila ta wuce gona da iri. Idan bamu dakatar da hare-haren da take kaiwa ba, ko shakka babu wata rana garemu zata fado”
Shugaba Erdogan ya kara da cewa Turkiyya shirye take ta yi ruwa da tsaki a cikin ko wane irin mataki da Majalisar Dinkin Duniya za ta dauka domin kawo karshen rikicin.
Kawo yanzu na zanta da shugabanin kasaseh 19 inda muka yiwa juna barka da sallah tare da tattaunawa akan maslahar Falasdin.
Shugaba Erdogan ya kuma ja kunnen Kungiyar Tarayyarv Kasasshen Musulmi na (OIC) da cewa idan basu dauki kwararan matakia akan Isra’ila ba za ta kasance tamkar kyanwar Lami. A yau ranar Lahadi ne dai Kungiyar Tarayyar Kasashen Musulmi za ta gudanar da taron koli akan cin zarafin da Isra’ila ke yiwa Falasdinawa.