Kusan ƙasashe 200 ne suka hallara a taron ƙolin sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana a babban birnin Azerbaijan Baku, wanda a bana ya mayar da hankali kan tara biliyoyin daloli, domin samar da kuɗaɗen samar da makamashin da baya da illa ga muhalli da kuma takaita barnar da gurɓatatcen hayaƙi ke yiwa muhalli.
Game da samar da kuɗaɗen yaki da sauyin yanayi, dole ne a bayar da kuɗaɗen, ko kuma matsalar ta shafi rayuwar ɗan Adam, lokaci na ƙara ƙure mana don takaita tsananin zafi a duniya da ya ƙaru zuwa ma'aunin Celsius 1.5.
Kamar yadda aka tsara a taron, yau ce ranar da shugabannin ƙasashe za su hallara don tattauna yadda za a samar da mafita game da matsalar sauyin yanayi, sai dai da dama daga cikin su basu halarci taron ba.
Shugaba Joe Biden na Amurka na daga cikin waɗanda basu halarci taron ba, inda takwaransa na China Xi Jinping ya aike da mataimakiyarsa, haka nan shugaban India Narendra Modi da Emmanuel Macron na Faransa da shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, duk ba a gansu ba a zauren taron.
Masana kimiya dai sun yi hasashen cewa, wannan shekara ce za ta zama mafi tsananin zafi a tarihi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI