Shugaban Kwamitin Kasa da Kasa a Samar da Adalci da zaman Lafiya a Kudus Manuel Musellem, ya bayyana cewar matakin da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya dauka na sake mayar da Hagia Sophia Masallaci mataki ne da zai kara darajar da kiman ginar a doron kasar.
Musellem wanda limamin darikar Katolika ne ya yada wani bidiyo a shafukansa na sadar da zumunta inda yake kira ga 'yan uwansa Kiristawa da cewa,
"Ku lura da cewa shugaba Erdoğan ya dauki matakan kara daraja da kiman Cocunanmu"
Musellem da ke kira ga Kiristawan duniya da su yi farin cikin mayar da Hagia Sophia Masallaci domin bautawa Allah da Turkiyya ta yi ya kara da cewa,
"Shugaba Erdoğan ya mayar da gurin ajiye kayan gargajiya da kowa ke birgina a cikinsa gurin bauta da ambaton Ubangiji, wannan abin yabawa ne da kauna"
A yayinda Musellem ke tunatar da cewa a Spain da wasu kasashen Larabawa an mayar da wasu Cocuna Masallatai, an kuma mayar da wasu Masallatai Cocuna; ya kara da cewa an taba lokacin da ake karanta Injila a cikin Hagia Sophia, a halin yanzu kuma za'a ci gaba da karatun Alkur'ani mai tsarki a cikinsa.