Limamin Babban Masallacin Hagia Sophia mai dinbin tarihi dake birnin Istanbul ya bayyana cewa zai ajiye limanci domin komawa yin hidima a harkokin ilimi.
Mehmet Boynukalin, wanda ya kasance limamin Masallacin Hagia Sophia mai shekaru 1,500 a birnin Istanbul ya nemi ya ajiye limancinsa kuma an amince masa.
Zai ci gaba da aiki a fannin ilimi a Jami’ar Kimiyyar Marmara dake kasar Turkiyya.
Boynukalin ya kasance yana hidima a Masallacin tare da wasu mataimaka biyu tun daga watan Yuli na shekarar bara, a lokacin da aka mayar da Hagia Sophia Masallacin .