A yayin wani aikin tiyata a Ostiriya, likitoci sun yanke cinyar dama ta wani tsoho dan shekaru 82 maimakon ta hagu da ya kamata su yanke.
A asibitin dake yankin Freistadt an yi aika-aika da babban kuskure a yayin aiki ga tsohon mai shekaru 82.
Tsohon na da cututtuka da dama wadanda suka shafi cinyoyinsa dukka biyu, amma lamarin ya kai ga sai an yanke cinyar hagu.
Amma sakamakon kuskuren da aka yi kafin tiyatar wajen nuna wacce cinya za a yanke, sai aka yanke masa cinyar dama maimakon ta hagu.
Asibitin ya sanar da cewa, kuskuren ya afku ne sakamakon yanayin dimuwa da aka shiga a jere.
An sanar da fara gudanar da bincike tare da hana irin wannan kuskure afkuwa a nan gaba.
Haka zalika ana ta kokarin kwantar da hankalin mara lafiyar.