Likitoci a India na zanga-zanga, bayan kashe abokiyar aikin su ta hanyar fyade

Likitoci a India na zanga-zanga, bayan kashe abokiyar aikin su ta hanyar fyade

Lamarin ya faru ne a garin Kolkata na ƙasar da ke da yawan jama’a.

Faya-fayan bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda dubban likitoci suka kwarara kan titunan garin na Kolkata da sauran sassan ƙasar, inda suke buƙatar gwamnati ta yi duk mai yiwuwa wajen kamo waɗanda suka aikata laifin tare da hukunta su, a cewar su wannan ne kadai hanyar da za’a yiwa matashiyar adalci.

Rahotanni sun ce an tsinci gawar matashinyar mai shekaru 31 a Juma’ar da ta gabata, inda gwaje-gwajen lafiya suka tabbatar da cewa sai da  aka yi mata fyade kafin a hallaka ta.

Kawo yanzu dai an kama wani matashi da ke aikin sa kai a rundunar ƴan sandan ƙasar da hannu cikin lamarin duk da dai ba’a kai ga kammala bincike ba.

Ƙididdiga ta nuna cewa likitoci sama da dubu 8 ne suka fita wannan zanga-zanga a Mumbai da jihar Maharashtra, lamarin da ya dakatar da aikin kiwon lafiya baki ɗaya.

A jihar New Delhi kuwa likitocin ne sanye da fararen kaya suka kwarara kan tituna, inda suke rera waƙoƙin tilastawa gwamnati kawo ƙarshen wannan cin zarafi.

Har yanzu dai gwamnatin ƙasar bata ce komai game da wannan zanga-zanga a hukumance ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)