Wani likitan kasar Turkiyya ya kirkiro kayan gwajin kwayar cutar Covid-19 ta auna fitsari.
Kwararren likitan Dkt. Mehmet Serhan Kurtulmus, ya bayyana cewa za'a iya gano kwayar cutar Sars Cov-2 ta auna fitsarin al'umma.
Kurtulmus ya bayyana cewa tun bayan bulluwar cutar Korona a Turkiyya a watan Maris din shekarar bara ne ya fara aikin gano kwayar cutar ta auna fitsari inda ya kammala a watan Nuwamba.
Kurtulmus ya kara da cewa bayan hukumar lafiya da hukumar magungunan kasar Turkiyya sun gwada amincin gwajin ne ma'aikatar lafiyar kasar ta amince dashi.Ya kara da cewa wannan abin gwajin ya fi wadanda ake amfani dasu tasiri kuma bayan gwaje-gwajen da aka yi an yada wannan abin gwajin ta wallafashi a wata mujallar kiwon lafiya ta matakin kasa da kasa.