Berri ya ce shawarwarin sun hada da kafa wani kwamiti da zai kula da aiwatar da kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701, wanda ya tanadi kwance damarar kungiyar Hizbullah tare da ficewa daga kan iyakar kasar da Isra'ila da ke gabar kogin Litani.
Kakakin ya ce tsarabe-tsaraben da aka gabatar musu ba za su aminta da su ba, amma tattaunawar za ta ci gaba da gudana cikin yanayi mai kyau.
Berri ya kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa akwai shawarwarin da suka kunshi tura dakarun NATO ko wasu dakaru zuwa cikin kasar Lebanon hadi da bayar da 'yancin walwala ga sojojin Isra'ila da ke cikin kasar.
Mutum 59 harin Isra’ila ya kasha a sassan kasar Lebanon, kamar yadda ma’akatar lafiya ta kasar ta tabbatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI