Lavrov ya yi magana kan dangantakar Rasha da EU

Lavrov ya yi magana kan dangantakar Rasha da EU

Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergey Lavrov da yake bayyana cewar kasarsa ba ta matsa daga Tarayyar Turai (EU) ba, ya ce "Brussels da gangan ta dagula tsarin alakar kasashen biyu." 

Lavrov da Ministan Harkokin Wajen Finlan, Pekka Haavisto sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa bayan tattaunawarsu a birnin St. Petersburg da ke Rasha.

Da yake nuna cewa dangantakar Rasha da Tarayyar Turai ta tabarbare, Lavrov ya ce,

"Brussels da gangan ta dagula tsarin alakar kasashen biyu." 

Kuma da yake bayyana cewa a shirye suke don magance matsaloli tare da EU, Lavrov ya ce,

"Dole ne mu kasance a shirye don ci gaban dukkan al'amuran. Zaɓin shi ne EU. Idan EU ta yanke shawarar inganta alaƙarta da Rasha, za mu kasance cikin shirin yin hakan." 

Lavrov ya kara da cewa, "Ba mu ƙaura daga Turai ba. Muna da abokai da yawa a Turai da ƙasashe masu irin wannan ra'ayi. Za mu ci gaba da haɓaka alaƙa da su a cikin tsarin abubuwan da suka shafi muradun juna." 

Ministan Harkokin Wajen Finlan, Pekka Haavista ya ce, "Yana da matukar muhimmanci a samo hanyoyin da za su tabbatar da tattaunawa da musayar ra'ayi tsakanin EU da Rasha." 


News Source:   ()