Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov wanda ya kai ziyarar aiki a Bosniya da Herzegovina, ya tattauna da takwararsa Bisera Turkovic a Sarajevo, babban birnin kasar.
Lavrov ya bayyana a wani taron manema labarai tare da takwararsa Turkovic cewa hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu zai ci gaba da karfafa.
Lavrov ya bayyana cewar halayyar Rasha da goyon bayanta za su ci gaba don kare yankuna da ikon Bosniya da Herzegovina.
Da yake bayyana cewar sun yanke shawarar kara karfin kasuwancin da sabon nau'in cutar corona (Covid-19) ya katse, Lavrov ya nuna gamsuwarsa da aikin kamfanonin Rasha a Bosniya da Herzegovina.
Turkovic ta ce tattaunawar tsakanin wakilan ta yi amfani kuma dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta yi kyau kuma ya kamata a bunkasa hadin gwiwa a fannoni daban daban.
Ta lura da cewa Rasha na goyon bayan 'yanci da ikon mallakar duk yankunan Bosniya da Herzegovina.