Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa, "Sakawa Turkiyya takunkumi da Amurka ta yi na nuni da tsagwaron halayyar girman kai wajen sabawa dokokin kasa da kasa."
Lavrov da ke ziyarar aiki a kasar Bosniya ya yi jawabi ga manema labarai.
Lavron ya ce, matakin takunkumin na Amurka kidahumanci ne kawai.
Ya ce "Sakawa Turkiyya takunkumi da Amurka ta yi na nuni da tsagwaron halayyar girman kai wajen sabawa dokokin kasa da kasa. Wannan abu ba zai taba amfanar da amurka ba, wadda kasa da ake hada kai da ita wajen gudanar da aiyuka a duniya da suka hada da sha'anin tsaro da kere-keren kayan tsaro."