Shugaban kasar Labanon Michel Aoun ya ba da umarnin gabatar da rahoton take hakkin da Isra’ila ke aikatawa a kasarsa ga Majalisar Dinkin Duniya.
A cikin wata rubutacciyar sanarwa daga Fadar Shugaban kasar Lebanon, an bayyana cewa, sakamakon hare-haren sama da Isra’ila ta kai wa yankin Siriya da daddare, makamai masu linzami 2 sun fada kan yankin Labanon tare da haifar da asara ga wasu kayayyaki.
Shugaba kasar ya umarci mataimakin firaiminista kuma ministan tsaro Zeyne Aker, wanda ke aiki a matsayin Ministan Harkokin Wajen, ya sanar da Majalisar Dinkin Duniya cewa "cin zarafin da sojojin Isra'ila ke yi wa 'yancin kasar Lebanon na ci gaba"
Ya yi kuma kira ga MDD ta dauki mataki sabili da hakan ya sabawa kudurin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na 1701.