Kyrgyzstan za ta fara karbar wutar lantarki daga Turkmenistan

Kyrgyzstan za ta fara karbar wutar lantarki daga Turkmenistan

Kyrgyzstan za ta shigo da wutan lantarki kilowatt miliyan 501 da dubu 900 daga Turkmenistan.

A cikin sanarwar da Ma'aikatar Makamashi da Masana'antu ta Kyrgyzstan ta fitar, an bayyana cewa ministan makamashi da masana'antu Doskul Bekmurzayev da ministan makamashi na Turkmenistan Carmirat Purcekov sun sanya hannu kan yarjejeniyar fitar da wutar lantarkin.

Dangane da haka, Kyrgyzstan za ta shigo da wutan lantarki kilowatt miliyan 501da dubu 900 daga Turkmenistan zuwa karshen shekara.

A yayin ziyarar aiki da shugaban Kyrgyzstan Sadir Caparov ya kai Turkmenistan a watan Yuni ne aka yi yarjejeniyar shigo da wutar lantarkin.


News Source:   ()