An sanar da cewa kwararar ruwa sanadiyar tsananin ruwan sama kamar da bakin kwarya ta yi sanadiyar rayukan mutum biyu a jihar Kumamoto dake kasar Japan.
Sanarwar ta kara da cewa kwararar ruwan ta yi kuma sanadiyar rushewar gadaje, faduwar bishiyoyi da rushewar gidaje da dama.
Lamarin ya haifar da mutuwar mutum biyu da kuma batar wasu mutum takwas.
A jihohin Kumamoto da Kagoşhima an kwashe mutum dubu 203 inda aka basu masauki, haka kuma an dakatar da kai-kawon jirgin kasar Shinkansen.
Bayan taron da firaiministan kasar Abe Shinzo ya yi ya bayar da umarnin kai kayayyakin agajin gaggawa ga al'umman jihar Kumamoto.
An dai tura ma'aikatan agajin gaggawa 450 da 'yan sanda 120 a yankin da lamarin ya afku.