Sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a yankunan Indiya daban-daban, kwarankwatsa ta fado tare da kashe mutane 116.
Jaridar India Today ta bayyana cewar gwamnati jihar Bihar ta sanar da mutuwarmutane 92 tare da jikkatar wasu 20 sakamakon kwarankwatsar da ta fado a loakcinda ake tafka ruwan sama.
Haka gwamnatin jihar Uttar Pradesh ta ce mutane 24 ne suka rasa rayukansu yayinda wasu 12 suka jikkata sakamakon fadowar kwarankwatsar.
Gidaje da dama sun lalace sakamakon mamakon ruwan saman.