Kwarankwatsa ta tarwatsa daurin aure a Bangaladesh

Kwarankwatsa ta tarwatsa daurin aure a Bangaladesh

An sanar da cewa kwarankwatsa da ta afkawa wurin daurin aure a Bangladesh ta yi sanadiyar mutuwar mutane 17.

Kwarankwatsa da ta afkawa al'ummar da ke kokarin kare kanta daga guguwar da ta barke ​​a lokacin daurin aure a garin Shibganj a yankin Chapainawabganj ta kashe rayuka 17 cikin 'yan dakikoki kadan.

Duk da dai masifar ba ta shafi amarya ba jami'ai sun ce ango ya tsira amma da raunuka.

Kwarankwatsa tana haddasa mutuwar daruruwan mutane a kowace shekara a Bangladesh, kasar dake  kudancin Asiya.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe tsawon mako guda ana yi a yankin Bazar na Cox ya yi sanadiyyar mutuwar kusan mutane 20 wadanda 6 daga cikinsu 'yan gudun hijira ne na Arakan.

Wasu masana sun bayyana cewa shuka daruruwan dubunnan dabino don rage tasirin canjin yanayi ya haifar da karin  kwarankwatsa da ya haifar da karin mace -mace a kasar.


News Source:   ()