Kwamitin Sulhu ya amince da matsayar Amurka kan rikicin Ukraine

Kwamitin Sulhu ya amince da matsayar Amurka kan rikicin Ukraine

Wannan kudurin na nuni da yadda Trump ke ci gaba da fifita manufofin Amurka kan batun Ukraine da kuma nanata matsayarsa na sasantawa da Rasha, saɓanin gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Joe Biden da ta jagoranci shirin tallafa wa Ukraine a lokacin yaƙin.

Jakadan Rasha na Majalisar Ɗinkin Duniya Vassily Nebenzia ya amince da abin da ya kira, sauyi mai cike da ma’ana da tarihi wato matsayin Amurka kan rikicin, na samar da zaman lafiya.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya mai mambobi 15 ya kasance cikin ruɗani a lokacin yaƙin, amma ba zai iya ɗaukar wani mataki ba saboda Rasha ta hau kujerar na-ƙi.

Sai dai matakin da Trump ya ɗauka na shiga tsakani ya sanya Ukraine da ƙawayenta na Turai shakku tare da fargabar cewa za a ware su a duk lokacin da aka zo batun tattauna yadda za a kawo ƙarshen yaƙin.

Tun da farko, babban taron ya zartas da kudurori guda biyu, ɗaya da Ukraine da ƙasashen Turai suka gabatar wanda kuma ya samu goyon baya, sai kuma wanda Amurka ta gabatar da ya samu kwaskwarima daga majalisar.

Kudirin da Amurka ta yi wa kwaskwarima ya samu kuri'u 93 a majalisar, yayin da kasashe 73 suka ƙaurace wa kaɗa kuri’a, inda takwas kuma suka ƙi amincewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)