Kwamitin karɓar mulkin Trump na shirin ganin Amurka ta fice daga WHO

Kwamitin karɓar mulkin Trump na shirin ganin Amurka ta fice daga WHO

Tun a shekarar 2020 ne Trump ya ƙirƙiri batun janyewar ƙasar daga hukumar lafiya ta duniya WHO, to sai dai bayan watanni 6, shugaba Joe Biden da ya karɓi ragamar mulkin Amurkan ya janye batun.

A cewar Lawrence Gostin, farfesan da ke kula da bangaren kiwon lafiya a jami’ar Georgetown da ke birnin Washington, kuma daraktan cibiyar tattara bayanai dangane da dokokin lafiya a ciki da wajen Amurka, ya ce ya na da yaƙinin cewa a ranar da Donald Trump zai soma wa’adi na biyu a shugabancin Amurka, toh tabbas zai tabbatar da manufarsa kan batun ficewar ƙasar daga WHO.

Financial times da ake wallafawa a Amurkan ce jarida ta farko da ta wallafa batun shirin, tare da bayyana sunayen ƙwararru 2 da suka gasgata hakan, ciki har da Ashish Jha, tsohon jami’in fadar White house da ke kula da ayyukan taƙaita yaɗuwar annobar COVID-19.

Wannan batu dai ya zo ɗaya da daɗaɗɗen caccakar da Trump ke yi wa yanayin tsarin hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya, kuma ya ƙudiri aniyar kawo gaggarumin sauyi wajen tunkarar harkokin lafiya a Amurka tare da ware kasar daga kasashen duniya masu kokarin yaki da barkewar annobar cuta.

Trump dai ya zaɓi manyan masu caccaka daga hukumar dan jagorantar bangaren kiwon lafiya a Kasar, daga ciki har da Robert F. Kennedy Jr, wani kwararre a bangaren lafiya da bai yarda da riga kafi ba, kuma ke Shirin zama sakataren harkokin kiwon lafiya da kula da ayyukan dan adam, kuma ke as ido a kan duk wasu cibiyoyin kiwon lafiya a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)