Kwamandan Rundunar Sojojin Saman Girka ya yi murabus

Kwamandan Rundunar Sojojin Saman Girka ya yi murabus

A Girka an ba da rahoton cewa Kwamandan Rundunar Sojojin Sama, Manjo Janar Giorgos Kumentakis ya yi murabus daga mukaminsa.

Dangane da labaran kafofin watsa labarai na Girka, an bayyana cewa Kumentakis ya gabatar da wasikar murabus bayan Babban Taron Majalisar Soja wanda Babban Hafsan Hafsoshin Girka Konstandinos Floros ya jagoranta.

A cikin labaran an yi iƙirarin cewa murabus ɗin Kumentakis, wanda aka ce yana da alhakin kula da jirage masu saukar ungulu irin na Chinok, yana da alaƙa da sukar da aka yi cewa jiragen soja basu bayar da gudummawa sosai ga ƙoƙarin kashe gobarar da aka yi ba.

Har yanzu babu wata sanarwa da aka bayar kan ko an amince da murabus din Kumentakis.


News Source:   ()