Kwalera ta yi sanadiyar rayukan mutane fiye da 800 a cikin kimanin watanni shida

Kwalera ta yi sanadiyar rayukan mutane fiye da 800 a cikin kimanin watanni shida

Mutane 83 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar kwalara a jihar Kaduna ta Najeriya.

Sakataren Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kaduna (NCDC), Dr. Hamza Ibrahim Ikara, a cikin bayanin sa, ya bayyana cewa cutar kwalara ta bazu zuwa yankuna 19 na jihar Kaduna,

"Zuwa yanzu, mutane dubu 1,120 aka tabbatar sun kamu da cutar kwalara, kuma mutane 83 sun mutu sakamakon barkewar cutar." 

Da yake bayyana cewa an tura kungiyoyin likitoci zuwa yankuna 19 don shawo kan lamarin, Ikara ya ce annobar ta bazu saboda tushen ruwa kuma za a samar da ruwa mai dauke da sinadarin chlorine don magani.

Fiye da mutane 800 ne suka mutu sakamakon cutar kwalara a fadin Najeriya tun daga watan Janairu.


News Source:   ()