An sanar da cewa wani kwale-kwalen masu kamun kifi ya kife lamarin da ya haifar da batar mutum 11 a kasar Indonesiya.
Dangane ga labaran da suka fito daga kanfanin dillancin labaran Kompas a tsibirin Java da Sumatra kusa da bakin ruwan Sunda wani kwale-kwale dauke da masunta 16 ya kife sanadiayar da iska mai karfin da ta rinka kada ruwa.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar (BASARNAS) ta kubutar da mutum 6 inda ake cigaba da neman sauran 10.
Mahukunta sun bayyana cewa ana cigaba da neman wadanda suka batan a tsibirin Rakata.