An sanar da cewa kıfewar wanı kwale-kwale dauke da 'yan gudun hijira 26 daga Tunusiya zuwa Italiya ya yi sanadiyar batar mutane 25.
Kamar yadda ma'aikatar tsaron Tunisiya ta sanar a rubuce Tunus wani kwale kwale dauke da yan gudun hijira da ya taso daga bakin gabar Safax ya kife a gabar garin El-Mehdiye dake kudancin kasar.
Hukumar Sojin Ruwan Tunisiya ta bayyana fara aikin ceto wadanda suka batan. Kasahen Libiya da Tunisiya sun kasance kasashen da 'yan gudun hijira daga kasashen Afirka ke bi domin shigewa Turai.