Kwale-kwale dauke da bakin haure 175 ya kife a Tunisiya

Kwale-kwale dauke da bakin haure 175 ya kife a Tunisiya

Jirgin ruwan dauke da bakin haure 175 wadanda ke neman shiga Turai ba bisa ka'ida ba ya nitse a mashigar garuruwan kudu da gabashin Tunisiya.

Husameddin Cebabli, kakakin rundunar tsaron kasar ta Tunusiya, ya sanar da cewa an ceto bakin haure 175 wadanda ke neman shiga Turai ba bisa ka'ida ba, wadanda kwale-kwalensu suka nitse a gabar tekun dake kudancin Kabis, Djerba da Cercis da arewa masu gabashin Nabil da kuma Monastir dake gabashin kasar a ranar 21 ga Yuli da kuma 22.

Cebabli ya bayyana cewa rundunonin tsaron kasar sun kame mutane 54 wadanda ke shirin tsallakawa zuwa Italiya daga Bizerte da Binarus a arewa, Monastir a gabas da Mednin a kudancin kasar.

Kakakin Cebabli bai bayar da bayanai game da kasashen da bakin hauren suke ba.


News Source:   ()