Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyar annobar kwalara a jihar Bauchi dake Najeriya ya kai 42.
Shugaban Hukumar Inganta Lafiya ta (PHCDA) reshen jihar Bauchi Dr. Rilwan Mohammed ya ce tun daga ranar 25 ga watan Mayu, mutane 2,874 suka kamu da cutar kwalara a sassa daban-daban dake yankin.
Muhammed ya ce tare da karin wasu mutane 5 a cikin kwanaki hudu da suka gabata, adadin mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar a yankin ya karu zuwa 42 a cikin wata guda, kuma ana jinyar mutane 300.
Da yake lura da cewa an aike da magunguna na gaggawa da kayayyakin kiwon lafiya zuwa yankunan da aka ga cutar, Muhammed ya yi kira ga mazauna yankin da su kiyaye da cutar.