A shirin da ake gudanarwa na samun zaman lafiya a kasar Turkiyya wani dan ta'addan YPG/PKK ya tuba ya mika wuya ga jami'an tsaro a yankin Mardin.
Kamar yadda kafafen jami'an tsaron yankin suka sanar wani dan ta'adda da ya tuba ya tsere daga gungun 'yan ta'addan na PKK/KCK/PYD/YPG inda ya mika wuya ga jami'an tsaro.
Dan ta'addan mai lakabi Z.O, da ake kira "Zindan Amed", wanda aka shawo kansa a cikin ayyukan da aka gudanar a wannan yanayin, ya mika wuya ga jami'an tsaro ba tare da makamai da kayan aiki ba.
Z.O, wanda ya shiga kungiyar ta'adda a shekarar 2015 daga Mardin, ya kasance wanda ake nema da laifin aikata miyagun laifuka.