An bayyana cewa a daren yau duniya za ta fuskanci kusufin wata da aka yiwa taken "Super Moon" inda rana za ta kama watar baki dayanta.
Kasancewar kusafin zai bayyana ne a cikin watan Mayis da muke ciki an radawa wanna. suna da "Blood Moon" wanda ke nuni da launin ja na watan Mayun.
Masana ilimin sararin samaniyya sun bayyana cewa za'a iya ganin kusufin wata a yammacin yankin Arewacin Amurka, Mexico, kasashen Amurka ta tsakiya, yammacin Peru, kudu da Chile da Argentina, gabashin Australia, New Zealand, da tsibiran da ke gabashin Tekun Fasifik.