A duniya baki daya mutane sama da dubu 861 da 280 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Corona (Covid-19). Ya zuwa yanzu cutar ta kama adadin mutane sama da miliyan 25 da dubu 906, adadin wadanda suka warke kuma ya haura mutane miliyan 18 da dubu 200.
Mutane 1,045 sun sake mutuwa a Indiya wanda ya kawo adadin wadanda cutar ta kashe a kasar zuwa mutane dubu 66,333. A awanni 24 da suka gabata cutar ta kama mutane dubu 78 da 357, inda jimillar wadanda ta kama a kasar ya kai mutane miliyan 3 da dubu 769 da 523.
A nahiyar Afirka kuma, cutar ta yi ajalin mutane dubu 30,104. A nahiyar gaba daya kuma cutar ta kama jimillar mutane miliyan 1 da dubu 264 da 417. Afirka ta Kudu ce ke kan gaba a nahiyar Afirka wajen rasa rayuka da mutane dubu 14,263 sai Masar da dubu 5,421 inda Aljeriya ke biye mata baya da dubu 1,518.
A kasar Mauritius ba a sake samun wanda cutar ta kama ba, inda a kasar Eritiriya kuma babu wanda ya mutu daga Corona.