Kusan mutane miliyan 25.5 corona ta kama a duniya baki daya

Kusan mutane miliyan 25.5 corona ta kama a duniya baki daya

A duniya baki daya, annobar Corona (Covid-19) ta yi ajalin mutane sama da dubu 850 da 630. Adadin wadanda cutar ta kama kuma ya haura miliyan 25 da dubu 390. Wdanda suka warke kuma sun haura miliyan 17 da dubu 709.

A awanni 24 da suka gabata Corona ta yi ajalin mutane 971 a Indiya.  Adadin wadanda cutar ka kashe a kasar ya kai mutane dubu 64,469. An kuma samu karin mutane dubu 78,512 da cutar ta kama a kasar a awanni 24 da suka gabata, wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu zuwa miliyan 3 da dubu 621 da 245.

A Iraki kuma cutar ta Corona ta sake yin ajalin mutane 68 wanda adadin wadanda suka mutu ya kai dubu 6,959. Sanarwar da aka fitar daga Ma'aikatar Lafiya da Tsara Muhalli ta ce a awanni 24 da suka gabata an samu karin mutane dubu 3,731 dauke da Corona wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu zuwa dubu 231,177.

A nahiyar Afirka kuma karin mutane 161 sun sake mutu wanda ya kawo adadin wadanda Corona ta kashe zuwa mutane dubu 29,633. Karin mutane dubu 8,463 sun kamu da cutar wanda ya kawo adadin masu dauke da ita a nahiyar Afirka zuwa miliyan 1 da dubu 25 da 375. Ya zuwa yanzu Afirka ta Kudu ce take da mafi yawan mutuwa daga Corona a Afirka da mutane dubu 14,028 sai Masar da ke dubu 5,399 inda Aljeriya ke biye mata baya da dubu 1,501.


News Source:   ()