Kusan mutane miliyan 23 ne suka warke daga Corona a duniya

A duniya baki daya annobar corona (Covid-19) ta yi ajalin mutane dubu 965 da 630. Adadin wadanda cutar ta kama ya kai sama da mutane miliyan 31 da dubu 273, wadanda suka warke kuma sun kusa ka, wa mutane miliyn 23.

A awanni 24 da suka gabata mutane 157 sun sake mutuwa a Indiya wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa mutane dubu 87,933. Wasu mutanen su dubu 86,961 sun sake kamuwa da cutar inda adadin wadanda suka kamu ya kai mutane miliyan 5 da dubu 491 da 410.

An bude wajen yawon bude na Tac Mahal da aka rufe watanni 6 da suka gabata sakamakon cutar ta Corona.

A Iran mutane 177 sun sake mutu sakamakon kamuwa da corona wanda ya kawo adadin wadanda annobar ta kashe zuwa mutane dubu 24,478 a kasar. Karin mutane dubu 3,341 sun kamu da cutar wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu zuwa dubu 425,481.

A Rasha mutane dubu 19,489 ne suka mutu inda aka sake samun mutane dubu 6,196 a rana guda. ya zuwa yanzu jimillar mutane miliyan 1 da 109 da 595 cutar ta kama a Rasha.

A Iraki kuma mutane 64 sun sake mutuwa inda ya zuwa yanzu jimillar mutane dubu 8,555 suka mutu. Wadanda suka kamu kuma sun karu da dubu 3,438 inda suka kama dubu 319,035. A Labanan mutane 297 ne suka mutu, a karon farko an samu mutane sama da dubu daya sun kamu inda adadin wadanda corona ta kama a kasar ya karu zuwa dubu 29,303.


News Source:   ()