Kusan mutane miliyan 20 ne suka warke daga cutar Corona a duniya baki daya

A duniya baki daya, annobar Corona (Covid-19) ta yi ajalin mutane sama da dubu 887,596. Ta kama jimillar mutane sama da miliyan 27 da dubu 296, inda adadin wadanda suka warke kuma ya kusa kai wa miliyan 20.

A awanni 24 da suka gabata a Indiya mutane 16 sun mutu, wanda ya kawo adadin wadanda cutar ta kashe a kasar zuwa dubu 71,642. Mutane dubu 90,802 sun sake kamuwa inda adadin wadanda suka kamu ya tashi zuwa miliyan 4 da dubu 204 da 613.

A nahiyar Afirka kuma mutane dubu 31,357 corona ta kashe daga cikin sama miliyan 1 da dubu 305 da ta kama.

Afirka ta Kudu ce ke kan gaba wajen yawan rasa rayuka a Afirka da mutane dubu 14,889 inda Masar ta ke biye mata baya da dubu 5,530 sai Aljeriya da dubu 1,556.

A kasar Mauritius babu sauran wanda ya ke dauke da cutar Corona, sannan a kasashen Seychelles da Eritiriya kuma ba a samu rahoton rasa rai ba.


News Source:   ()