Sama da mutane dubu 982 ne suka rasa rayukansu sakamakon annobar corona a duniya baki daya. Ya zuwa yanzu cutar ta kama mutane miliyan 31 da dubu 101, wadanda suka warke kuma sun kai haura mutane miliyan 23 da dubu 682.
A Indiya adadin wadanda cutar ta covid-19 ta yi ajali sun kai sama da mutane dubu 91,173. Haka zalika wadanda cutar ta kama a kasar sun tashi zuwa miliyan 5,8.
A nahiyar Afirka kuma mutane 209 sun sake mutu inda adadin wadana corona ta yi ajali ya kama mutane sama da dubu 34 da 587. A awanni 24 da suka gabata cutar ta kama mutane dubu 8,813 wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu zuwa miliyan 1 da dubu 436. Afirka ta Kudu ce ke a kan gaba wajen samun rasa rayuka da mutane dubu 16,206 sai Masa da dubu 5,822 inda Morokko ke biye mata baya da 1,918.