Kungiyoyin jin kai na kasar Turkiyya sun raba ababen layya a kasashe 27

Kungiyoyin jin kai na kasar Turkiyya sun raba ababen layya a kasashe 27

Kungiyoyin bayar da tallafi da agajin gaggawa na kasar Turkiyya sun raba dabbobin layya guda 30, 000 a kasashe 27 a fadin duniya.

Duk da matsalar kai kawo sabili da kwayar cutar Covid-19 kungiyar bayar da agaji ta Cansuyu dake Istanbul ta shirya mika hannunta ga akl’umman Musulmi har miliyan 1.5 kamar yadda shugaban tawagar kungiyar Mustafa Koylu ya shaidawa kanfanin dillancin labaran Anadolu.

Layya dai na tunatar da yunkurin Annabi Ibrahim wanda ya yi alkawarin layya da dansa amma Allah (SWT) ya sauya masa da rago.

A wannan shekarar kungiyar Cansuyu ta zabi kasashen maras karfi kamarsu Yaman, yankin Rakhine dake Myanmar, Yankin Bangsamoro mai zaman kansa a Philippines.

Haka kuma zuwa Afirka sun raba ababen layyan a kasashen Mauritania, Chad, Cameroon, Niger, Benin, Mali, Burundi, Somaliya, Ivory Coast, Kenya, Burkina Faso, Tanzania, Guinea, Senegal, Zimbabwe, da Zambia."


News Source:   ()