Kungiyoyin daba na amfani da fyade amatsayin makamin yaki a Haiti -HRW

Kungiyoyin daba na amfani da fyade amatsayin makamin yaki a Haiti -HRW

Sanarwar ta ƙara da cewa yanzu haka ƙungiyoyin dabar sun ɗauki wani sabon salo na yin amfani da fyaɗe a matsayin nau’in rikicin.

A cewar jami’in  bincike na hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta Human Rights Watch, Nathalye Cotrino, abin takaci ne yadda ƴan dabar su ke yi wa mata da ƙananan yara fyaɗe, inda ta ce sun samu tattaunawa da waɗanda aka ci zarafinsu, da kuma wasu jami’an kare haƙƙin ɗan adam.

Ta ce daga watan janairu zuwa Oktoban 2024, kusan ƙananan yara da mata dubu 4 ne aka ci zarafinsu.

Wata uwa mai shekaru 25 ta ce wasu mutane 4 da ke tafiya a gungu, sun yi mata fyaɗe yayin da ta ke ƙoƙarin samar wa ƴaƴanta ruwan sha, inda ta bayyana cewa a baya ba su saba ganin haka ba, amma a yanzu lamarin ya sauya.

Majalisar ɗinkin duniya ta bayyana cewa aƙalla mace 1 ake kashewa a duk mintuna goma sanadiyyar cin zarafi a faɗin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)