Kungiyoyin bada agaji na musulmin Kanada sun aikawa firaiministan Justin Trudeau wasika don bincike akan yukurin kara musu haraji abinda suka kira rashin adalci kamar yadda kafofin yada labaran Kanada suka ruwaito.
Wani rahoto da aka fitar kwanan nan daga Kungiyar Kula da 'Yancin Dan Adam ta Kasa da Kasa ta ce Hukumar Kula da Haraji ta Kanada (CRA) ta shiga cikin jami'an tsaron kasar don kai wa kungiyoyin agaji na Musulmi hari.
Lokacin da kungiyoyin suka rasa matsayinsu na sadaka, masu bada gudummawa ba za su iya kara bayar da kudade ba sai sun biya haraji ba, wanda ke haifar da raguwar gudummawar.
Wasikar da aka aika a ranar Laraba kungiyoyin 129 ne suka sanya hannu, ciki har da Majalisar Musulmin Kanada, Cibiyar Edmonton Islamic Center, Masallacin Musulmin London da kungiyoyin 'yanci na jama'a, a cewar jaridar Globe da Mail.
Kamfanin dillancin labaran Anadolu (AA) ya ba da rahoto a farkon wannan watan cewa CRA ta ware kungiyoyin agaji na Muslmai don binciken su kuma kungiyoyin agaji sun shirya neman Trudeau ya gudanar da bincike.