Kungiyar ta'addar DEASH ta kai wa Hashd al Shaabi hari

Kungiyar ta'addar DEASH ta kai wa Hashd al Shaabi hari

An sanar da cewa akwai mutanen da suka mutu a harin da kungiyar ta'adda ta DAESH ta kai wa Hashd al-Shaabi a arewacin Bagadaza babban birnin Iraki.

Kafafan yada labarai na cikin gida sun bayyana cewa, kungiyar ta'adda ta DAESH ta kai hari kan sansanin dakaru na 12 na Hashd al-Shaabi da ke yankin Tarimiye a Bagadaza.

An yi ikirarin cewa akwai mutanen da suka mutu a harin, ciki har da mataimakin kwamandan sansanin, daga cikin Hashd al-Shaabi.

Gwamnatin Iraki da Hashd al-Shaabi har yanzu ba su fitar da wata sanarwa game da harin ba.


News Source:   ()