Kungiyar hadin kan kasashen Musulmi (OIC) ta aminta da ta gudanar da taron koli domin tattaunawa akan yunkurin Isra’ila na mallake wasu yankunan Zirrin Gaza.
Wani jam’in da ya nemi a boye sunansa ya bayyanawa manema labarai cewar an aminta akan gudanar da taron ne bayan tattaunawar da ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya yi da wasu takwarorinsa ta wayar tarho.
Ministocin harkokin kasashen wajen mambobin kungiyar ta OIC ne kawai zasu halarci taron da kawo yanzu ba’a saka rana ba.
Gwamnatin Falasdin za ta mika kudurinta ga hukumar ta OIC bayan an kammala bukukuwan sallar Eid al-Fitr, wanda zai kasance tsakanin ranakun 24-26 ga watan Mayu.
Isra'ila na son kwace wasu sassan Zirrin Gaza a ranar 1 ga watan Yuli kamar yadda aka amince tsakanin Firayim Minista Benjamin Netanyahu da abokin hamayyarsa Benny Gantz na jam'iyyar Blue da White.
Wannan yunkurin na Isra’ila dai ya janyo tir da yin Allah wadai daga hukumomin kasa da kasa da dama.
Yankin Zirrin Gaza ya kunshi gabashin Jarusalam inda dokar kasa da kasa ta bayyana an mamaye, lamarin dake nuna cewa Yahudawan dake yankin suna zama ne ba bisa ka’iada ba.
A ranar Talata shugaban Falasdin Mahmoud Abbas ya sanar da kawo karshen dukkan wata yarjejeniya da suka hada da na tsaro tsakanin kasarsa da Isra’ila da kuma ma da Amurka.