Kungiyar D-8 ta jinjinawa Turkiyya

Kungiyar D-8 ta jinjinawa Turkiyya

Babban sakataren kungiyar D-8 na Tattalin Arziki da Hadaka Dato Ku Jaafar Ku Shaari ya bayyana cewa Turkiyya ta kara daukar matakan da zasu janyo masu saka hannayen jari a cikinta.

Dato Ku Jaafar Ku Shaari ya yabawa irin tsarukan da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kaddamar a kasarsa.

Ya bayyana cewa  “Ina ganin shugaba Erdogan ya fahince cewa sabbin tsarukan da suka inganta tattalin arziki, demokradiyya da doka zasu kara bunkasa kasar”

Bugu da kari kamar yadda Shaari ya shaidawa kanfanin dillacin labaran Anadolu.

Ya yi nuni da cewa bunkasar Turkiyya a cikin yan shekarun nan nada nasaba ga irin tsare-tsaren da aka kaddamar wadanda ke cigaba da janyo masu saka hannayen jari ga kasar.


News Source:   ()