Kotun Iraki ta bayar da umarnin a kamo Trump

Kotun Iraki ta bayar da umarnin a kamo Trump

Alkalin wata kotu a Iraki ya yanke hukuncin a kamo Shugaban Kasar Amurka Donald Trump, sakamakon kashe Shugaban Sojin Iran na Juyin Juya Hali Mai Kula da Kudus Kasim Sulaimani da Kwamandan Mayakan Hashdi Sha'abi Abu Mahdi Al-Muhadis.

Kotun da ke bincike da sauraren shari'ar Rusafa a Bagdad Babban Birnin Iraki ta sanar da cewa,

"Alkalin da ke bibiyar kisan gillan da aka yi wa Muhandis da abokansa, duba da hukunci na 406 na dokokin kotun hukunta manyan laifuka ta Iraki, ya yanke hukuncin a kamo Donald Trump."

A ranar 3 ga Janairun 2020 ne Amurka ta kai hari ta sama a filin tashi da saukar jiragen sama na Bagdad inda ta kashe Kasim Sulaimani da Muhandis.

Bayan kisan gillar, gwamnatin Iraki ta fara gudanar da bincike.

 


News Source:   ()