Rundunar ta musamman wadda aka ɗorawa alhakin bayar da kariya ga ma’aikatan ɓangaren lafiya musamman mata wadanda ke fuskantar cin zarafi a bakin aiki, samar da ita na zuwa ne bayan tsanantar cin zarafin da likitoci mata da sauran jami’an jinya ke fuskanta a bakin aiki, musamman na baya-bayan Dr Moumita Debnath mai shekaru 31 a jihar Kolkata ranar 9 ga watan nan.
Duk da yadda India ta yi ƙaurin suna wajen cin zarafin mata ta hanyar fyade da kuma kisan ba gaira-ba-dalili, kisan na Dr Moumita ya ja hankalin duniya musamman bayan da ƙungiyar likitocin ƙasar mai mambobi dubu 400 ta tsunduma yajin aiki baya ga shiga zanga-zanga, yayinda aka riƙa gabatar da mabanbantan gangami a ilahirin jihohin ƙasar.
Alƙaluma na nuna cewa kashi 60 cikin 100 na likitocin India Mata ne, dalilin da ya sanya ƙungiyar likitocin kira ga Firaminista Narendra Modi wajen ganin ya kafa runduna ta musamman da za ta bayar da akriya ga matan a bakin aiki baya ga ɗaukar matakan ladabtarwa ga duk wannan aka samu ga makamanciyar aika-aikar.
A shekarar 2012 ne India ta tsaurara dokar hukunci mai tsauri ga waɗanda aka kama da laifin fyade bayan kisan wata yarinya ƴar shekaru 12 a New Delhi bayan yi mata fyaɗe sai dai alamu na nuna cewa har yanzu.
Alƙaluman 2022 ya nuna yadda mata dubu 31 da 516 suka fuskanci fyaɗe a sassan India.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI