Kotu ta daure tsohon mijin Gisele Pelicot shekaru 20 bayan samunsa da laifin fyaɗe

Kotu ta daure tsohon mijin Gisele Pelicot shekaru 20 bayan samunsa da laifin fyaɗe

Kotu da ke kudancin birnin Avignon ta yankewa Dominique Pelicot hukuncin ne sakamakon ya amsa laifukan da ake zarginsa da aikatawa, bayan shafe watanni uku ana shari'ar da ta girgiza Faransa tare da mayar da tsohuwar matarsa ​​Gisele Pelicot jarumar mata.

Da yake zartar da hukuncin, Roger Arata  ya ce dole ne Dominique Pelicot ya yi zaman kashi biyu bisa uku na shekarun hukuncin da aka yanke masa, ko da kuwa za a yi masa afuwa.

A lokacin shari’ar dai Dominique Pelicot mai shekaru 72, ya amince cewa yana baiwa tsohuwar matarsa kayan maye ta fita hayyacinta, kafin ya gayyato mutanen da ya ke biya don suyi lalata da ita.

Haka nan kotun ta zartarwa mutane 50 da ke tsakanin shekaru 27 zuwa 74 da aka gurfanar da su tare Dominique Pelicot hukunci dai-dai da laifinsu, cikinsu har da wani da bayyi wa Gisele Pelicot fyaɗe ba, amma kuma ya tabbatar da cewar Dominique Pelicot ya taimaka masa wajen yiwa matarsa fyaɗe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)