Kotu ta bada umarnin tsawaita lokacin kada kuri'a a Pennsylvania

Kotu ta bada umarnin tsawaita lokacin kada kuri'a a Pennsylvania

Sakamakon wannan hukunci za'a ci gaba da bude tashoshin zabe na karin sa'oi 2 a yankin da tsohon shugaban kasa Trump ya samu kashi 70 na kuri'un da aka kada a zaben shekarar 2020.

Hukumar kula da zabuka a jihar ta gabatar da kara a kotu domin samun amincewar alkalai wajen karin lokacin saboda abinda suka kira tangardar na'urar zaben da aka samu wanda ya hana mutane da dama kada kuri'a.

Wannan ya sa kotun yankin ta amince da bukatar da kuma bada damar kara sa'oi 2 daga karfe 8 na dare agogon Amurka zuwa karfe 10 domin rufe tashoshin zaben.

Shugaban hukumar zaben yankin Michael Whatley ya tabbatar da umarnin kotun bayan karar da suka gabatar.

Ana saran hukuncin ya bai wa jama'a da dama damar sauke nauyin dake kan su ta hanyar kada kuri'un su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)